A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, sakamakon shigowar watan Rajab mai albarka, an gabatar muku da takaitattun bayanan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci game da shawarwari kan yadda za a yi amfani da wadannan kwanaki:
Menene Mafi Kyawun Aiki a Watan Rajab?
Mafi kyawun aikin da mutum zai yi a wannan watan, watakila shi ne istigfari. Haƙiƙa dukkanmu muna buƙatar mu yi istigfari kuma mu nemi mafaka ga Allah Maɗaukaki. Gafarar Ubangiji ita ce babbar ni'ima da Allah yake baiwa mutum a duniya da lahira. Hatta waliyan Allah, hatta Manzon Allah (S.A.W.A), ba su wadata ga barin gafarar Ubangiji ba:
"...Domin Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubinka da abin da ya jinkirta." (Suratul Fath: 2)
Wannan gafarar ta kasance ne saboda babu wanda zai iya sauke hakkin biyayya da bautar Ubangiji yadda ya kamata; istigfarin domin haka ne. "Ba mu bauta maka yadda ya kamata a bauta maka ba"; babu wanda zai iya sauke hakkin ibadar Ubangiji da hakkin bautar Allah yadda ya cancanta, komai kokarinsa. Wannan istigfarin saboda wannan ne. (16/01/2024)
Watan Rajab, Watan Addu’a ne da Tawassul
Watan Rajab dama ce mai kyau; watan addu'a ne, watan tawassul)' ne, watan maida hankali ne, kuma watan istigfari ne. Ya kamata mu kasance muna yin istigfari akai-akai. Kada wani ya yi zaton cewa ya wadata ga barin istigfari. Manzon Allah (S.A.W.A) yana cewa: "Lallai ana lulube zuciyata (da wani kalar yanayi), kuma lallai ni ina neman gafarar Allah sau saba'in a kowace rana."
Ba shakka Manzon Allah ma yana yin istigfari a kalla sau saba’in a rana. Istigfari na kowa ne; musamman mu da muke nutse a cikin hidimomin duniya da kazantarta. Istigfari yana tsarkake wani bangare na wannan kazanta kuma yana gusar da ita. Watan istigfari ne; insha Allah mu yi amfani da wannan dama. (24/06/2009)
Wannan Watan Shimfida ce ga Watan Sha'aban da Watan Ramadan
Yana da kyau mu yi amfani da damar wadannan kwanaki masu albarka na watan Rajab domin maida hankali kan wajibcin yin kokari a kowane mataki muke kuma a kowane aiki muke ciki. Kamar yadda ake iya fahimta daga addu’o’in watan Rajab, ra’ayina shi ne cewa wannan watan shimfida ne ga watan Sha’aban, sannan kuma watan Ramadan.
Wadannan watanni uku dama ce ta gyaran kai a tsawon shekara da kuma samar da guzuri da karfin da ake bukata don gudanar da rayuwa da makoma mai girma.
"Ya Allah ka shiryar da ni zuwa ga shiyar wadanda aka shiryar, ka azurta ni da kokarin masu ijtihadi..."
Kamar yadda muke karantawa a wannan watan, mai addu’a yana rokon Allah Ta’ala ta hanyar wadannan addu’o’in da ya haska masa da hasken shiriya; ya koya masa kokari da ijtihadi kuma ya ba shi ikon yin hakan, sannan ya kare shi daga gafala.
A wata addu’ar kuma ta wannan watan muna cewa:
"Ya Allah ina rokonka hakurin masu godiya gareka, da aikin masu tsoronka, da yakinin masu bauta maka." Wadannan su ne fukafukan da mutum zai iya tashi da su. Hakurin masu godiya, kokari da aikin masu tsoron Allah, da yakinin masu ibada; wadannan siffofi ne da muke rokon Allah ya ba mu a wannan watan, sannan kuma muna koyon darasi daga waɗannan addu’o’in cewa ya kamata mu samar da wadannan siffofi a cikin kanmu. (13/01/1993)
Your Comment